¹⁹ To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne. ²⁰ Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”
²¹ Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?”
Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.”
“Kai ne Annabin nan?”
Ya amsa ya ce, “A’a.”
²² A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”
²³ Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”
²⁴ To, waɗansu Farisiyawan da aka aika ²⁵ suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”
²⁶ Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba. ²⁷ Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”
²⁸ Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma.
²⁹ Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya! ³⁰ Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’ ³¹ Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”
³² Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa. ³³ Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ ³⁴ Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”
³⁵ Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa. ³⁶ Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
³⁷ Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.