¹⁴ Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, ¹⁵ wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. ¹⁶ Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. ¹⁷ Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, ¹⁸ don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. ¹⁹ Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.
²⁰ Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani. ²¹ Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.