¹⁸ Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. ¹⁹ Gama a rubuce yake cewa,
“Zan rushe hikimar mai hikima,
basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”
²⁰ Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? ²¹ Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. ²² Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, ²³ amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, ²⁴ amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. ²⁵ Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.
²⁶ ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. ²⁷ Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. ²⁸ Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, ²⁹ domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. ³⁰ Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. ³¹ Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.