Shugabannai Suna Gargadi Da Karfafa Gwiwa

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

1 Timoti 4: 1-16

¹ Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. ² Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. ³ Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. ⁴ Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, ⁵ domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a. ⁶ In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. ⁷ Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. ⁸ Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa. ⁹ Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. ¹⁰ Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya. ¹¹ Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa. ¹² Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. ¹³ Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. ¹⁴ Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka. ¹⁵ Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. ¹⁶ Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Me mu ka koya daga labarin nan game da zama shugabannai?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00