¹ A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. ² To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
³ Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. ⁴ Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. ⁵ Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
⁶ Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” ⁷ Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. ⁸ Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
⁹ Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. ¹⁰ Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
¹¹ Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. ¹² Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. ¹³ Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
¹⁴ Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, ¹⁵ bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. ¹⁶ Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. ¹⁷ Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, ¹⁸ su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. ¹⁹ Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
²⁰ Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” ²¹ Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. ²² Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” ²³ Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
²⁴ Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. ²⁵ Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.