¹⁵ Ubangiji Allah ya ɗauko mutumin ya sa shi cikin Lambun Eden domin yă nome shi, yă kuma lura da shi. ¹⁶ Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, ¹⁷ amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
¹⁸ Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
¹⁹ To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don yă ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. ²⁰ Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.
Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. ²¹ Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. ²² Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.
²³ Sai mutumin ya ce,
“Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana
nama kuma na namana.
Za a ce da ita ‘mace,’
gama an ciro ta daga namiji.”
²⁴ Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
²⁵ Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.