¹ A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. ² (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) ³ Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
⁴ Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne. ⁵ Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki. ⁶ Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi, ⁷ ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
⁸ Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare. ⁹ Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai. ¹⁰ Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane. ¹¹ Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. ¹² Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
¹³ Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,
¹⁴ “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama,
a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
¹⁵ Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”
¹⁶ Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami. ¹⁷ Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron, ¹⁸ duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa. ¹⁹ Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta. ²⁰ Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.