¹ Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, ² inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.
³ Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.”
⁴ Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’”
⁵ Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. ⁶ Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. ⁷ Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.”
⁸ Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”
⁹ Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. ¹⁰ Gama a rubuce yake,
“ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
su kiyaye ka da kyau;
¹¹ za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
¹² Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”
¹³ Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.
¹⁴ Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka. ¹⁵ Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.
¹⁶ Ya tafi Nazaret, inda aka yi renonsa. A ranar Asabbaci kuma, ya shiga majami’a kamar yadda ya saba. Sai ya miƙe don yă yi karatu. ¹⁷ Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,
¹⁸ “Ruhun Ubangiji yana kaina,
domin ya shafe ni,
in yi wa matalauta wa’azin bishara.
Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,
in kuma buɗe idanun makafi,
in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.
¹⁹ In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”
²⁰ Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. ²¹ Sai ya fara ce musu, “A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”
²² Duk suka yabe shi, suka yi mamakin kalmomin alheri da suke fitowa daga bakinsa. Suka yi tambaya, suna cewa, “Anya, wannan ba ɗan Yusuf ba ne?”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.