¹⁷ A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”
¹⁸ Ya amsa ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ ” ¹⁹ Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
²⁰ Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. ²¹ Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
²² Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
²³ Yesu ya amsa ya ce, “Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. ²⁴ Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa.”
²⁵ Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, “Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?”
Yesu ya amsa ya ce, “I, kai ma ka fada.”
²⁶ Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, “Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”
²⁷ Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, “Ku shassha daga cikinsa, dukanku. ²⁸ Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai. ²⁹ Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”
³⁰ Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.