³⁶ Sa’an nan Yesu ya tafi da almajiransa zuwa wani wurin da ake kira Getsemane, ya ce musu, “Ku zauna nan, in je can in yi addu’a.” ³⁷ Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. ³⁸ Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”
³⁹ Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”
⁴⁰ Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya tarar suna barci. Ya tambayi Bitrus ya ce, “Ashe, ba za ku iya yin tsaro tare da ni ko na sa’a guda ba? ⁴¹ Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
⁴² Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”
⁴³ Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci. ⁴⁴ Saboda haka ya sāke barinsu, ya yi addu’a sau na uku, yana maimaita iri abu guda.
⁴⁵ Sa’an nan ya komo wurin almajiransa, ya ce musu, “Har yanzu kuna barci kuna hutawa ba? Ga shi, sa’a ta yi kusa, an kuma bashe Ɗan Mutum a hannuwan masu zunubi. ⁴⁶ Ku tashi, mu tafi! Ga mai bashe ni nan yana zuwa!”
⁴⁷ Yayinda yana cikin magana, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya iso. Tare da shi kuwa ga taro mai yawa riƙe da takuba da sanduna, manyan firistoci da dattawan mutane ne suka turo su. ⁴⁸ To, mai bashe shi ɗin, ya riga ya shirya alama da su, “Wanda na yi masa sumba, shi ne mutumin; ku kama shi.” ⁴⁹ Da zuwansa, sai ya miƙe zuwa wurin Yesu ya ce, “Gaisuwa, Rabbi!” Sa’an nan ya yi masa sumba.
⁵⁰ Yesu ya amsa ya ce, “Aboki, yi abin da ya kawo ka.”
Sa’an nan mutanen suka matso, suka kama Yesu suka riƙe shi. ⁵¹ Ganin haka, sai ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu, ya zaro takobinsa ya kai wa bawan babban firist sara, ya fille masa kunne.
⁵² Sai Yesu ya ce, masa, “Mai da takobinka kube, gama duk masu zare takobi, a takobi za su mutu. ⁵³ Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba? ⁵⁴ Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yă faru?”
⁵⁵ A wannan lokaci sai Yesu ya ce wa taron, “Ina jagoran wani tawaye ne, da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? Kowace rana ina zama a filin haikali ina koyarwa, ba ku kuwa kama ni ba. ⁵⁶ Amma wannan duka ya faru ne don a cika rubuce-rubucen annabawa.” Sa’an nan dukan almajiran suka yashe shi suka gudu.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.