⁹ Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. ¹⁰ Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,
“Ceto na Allahnmu ne,
wanda yake zaune a bisan kursiyi,
da kuma na Ɗan Ragon.”
¹¹ Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, ¹² suna cewa,
“Amin!
Yabo da ɗaukaka,
da hikima da godiya da girma
da iko da ƙarfi
sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.
Amin!”
¹³ Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?”
¹⁴ Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.”
Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. ¹⁵ Saboda haka,
“suna a gaban kursiyin Allah
suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa;
kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu.
¹⁶ ‘Ba za su sāke jin yunwa ba;
ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.
Rana ba za tă buga su ba,’
ko kuma kowane irin zafin ƙuna.
¹⁷ Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;
‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’
‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.