³ Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
⁴ Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
⁵ Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu. ⁶ Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu. ⁷ Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’ ⁸ Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
⁹ Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
¹⁰ Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba? ¹¹ Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu. ¹² Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama? ¹³ Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum. ¹⁴ Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum, ¹⁵ don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”
¹⁶ Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. ¹⁷ Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. ¹⁸ Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. ¹⁹ Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. ²⁰ Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. ²¹ Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.