Menene Farashin Bin Yesu?

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

Mattiyu 10: 37-39

³⁷ “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; ³⁸ duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba. ³⁹ Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.

Markus 8: 34-38

³⁴ Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, “Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni. ³⁵ Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi. ³⁶ Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa? ³⁷ Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa? ³⁸ Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00