Menene Alkawuransa Ga Masu Bin Sa?

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

Afisawa 2: 1-10

¹ Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. ² Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. ³ Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. ⁴ Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, ⁵ ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. ⁶ Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. ⁷ Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. ⁸ Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. ⁹ Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. ¹⁰ Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

Romawa 5: 1-5

¹ Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, ² ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma farin ciki a begen ɗaukakar Allah. ³ Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; ⁴ jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. ⁵ Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00