Me Ya Gaya Mana Mu Yi?

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

Mattiyu 28: 16-20

¹⁶ Sa’an nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. ¹⁷ Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. ¹⁸ Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. ¹⁹ Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, ²⁰ kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”

Ayyukan Manzanni 1: 3-8

³ Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah. ⁴ A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai. ⁵ Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.” ⁶ Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?” ⁷ Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa. ⁸ Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00