⁴ Ku ji, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. ⁵ Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku. ⁶ Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. ⁷ Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. ⁸ Ku ɗaura su su zama alamu a hannuwanku, ku kuma ɗaura su a goshinku. ⁹ Ku rubuta su a dogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.