³⁶ To, ana nan, sai ɗaya daga cikin Farisiyawa ya gayyaci Yesu cin abincin yamma a gidansa, ya kuwa tafi gidan Bafarisiyen, ya zauna a tebur. ³⁷ Da wata mace wadda ta yi rayuwar zunubi a wannan gari ta ji Yesu yana cin abinci a gidan Bafarisiyen, sai ta kawo ɗan tulun turaren alabasta, ³⁸ ta kuma tsaya daga bayansa, wajen ƙafafunsa tana kuka, sai hawayenta sun fara zuba a ƙafafunsa. Sai ta goge su da gashin kanta, ta sumbace su, sa’an nan ta shafa musu turare.
³⁹ Da Bafarisiyen da ya gayyace shi, ya ga wannan, sai ya ce a ransa, “Da mutumin nan annabi ne, da ya san ko wace ce take taɓansa, da kuma irin macen da take, cewa mai zunubi ce.”
⁴⁰ Sai Yesu ya ce masa, “Siman, ina da abin da zan faɗa maka.”
Shi kuwa ya ce, “Malam sai ka faɗa.”
⁴¹ Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin. ⁴² Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”
⁴³ Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.”
Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.”
⁴⁴ Sai ya juya wajen macen, ya ce wa Siman, “Ka ga macen nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwa don ƙafafuna ba, amma ta wanke ƙafafuna da hawayenta, ta kuma goge su da gashin kanta. ⁴⁵ Ba ka yi mini sumba ba, amma tun shigowata a nan, macen nan ba tă daina sumbar ƙafafuna ba. ⁴⁶ Ba ka shafa mai a kaina ba, amma ta zubo turare a ƙafafuna.
⁴⁷ “Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”
⁴⁸ Sai Yesu ya ce mata, “An gafarta miki zunubanki.”
⁴⁹ Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
⁵⁰ Yesu ya ce wa macen, “Bangaskiyarki ta cece ki, ki sauka lafiya.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.