¹ Wata rana Yesu yana addu’a a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin addu’a, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”
² Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce,
“ ‘Ya Uba,
sunanka mai tsarki ne
mulkinka ya zo.
³ Ka ba mu kowace rana abincin yini.
⁴ Ka gafarta mana zunubanmu,
kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.
Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”
⁵ Sa’an nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, sa’an nan ya je wurinsa da tsakar dare ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, ⁶ domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ ⁷ Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ ⁸ Ina gaya muku, ko da yake ba zai so ya tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.
⁹ “Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. ¹⁰ Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.
¹¹ “Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, ¹² ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? ¹³ In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.