¹ “Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. ² Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. ³ Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. ⁴ Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
⁵ “Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. ⁶ Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. ⁷ In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. ⁸ Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
⁹ “Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. ¹⁰ In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. ¹¹ Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. ¹² Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. ¹³ Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. ¹⁴ Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. ¹⁵ Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. ¹⁶ Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. ¹⁷ Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.