Ikkilisiya Amaryar Kristi Ce

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

Afisawa 5: 25-32

²⁵ Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. ²⁶ Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. ²⁷ Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. ²⁸ Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. ²⁹ Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, ³⁰ gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. ³¹ “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” ³² Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.

Ruʼuya ta Yohanna 19: 6-9

⁶ Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki. ⁷ Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta. ⁸ Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.) ⁹ Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Me mu ka koya daga labarin nan game da zama ikkilisiya?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00