⁴ Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi ⁵ ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. ⁶ Gama a cikin Nassi an ce,
“Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona,
zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja,
wanda kuma ya dogara gare shi
ba zai taɓa kunyata ba.”
⁷ A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba,
“Dutsen da magina suka ƙi
ya zama dutsen kusurwar gini,
⁸ kuma,
“Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe
kuma fā ne da yake sa su fāɗi.”
Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.
⁹ Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki. ¹⁰ Dā ku ba mutane ba ne, amma yanzu ku mutanen Allah ne; Dā ba ku karɓi jinƙai ba, amma yanzu kun karɓi jinƙai.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.