⁵ “Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’ ⁶ Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki. ⁷ Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku. ⁸ Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci, ⁹ a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba; ¹⁰ a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba; ¹¹ a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.
¹² “Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba. ¹³ Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna. ¹⁴ Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku. ¹⁵ Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.