³⁶ “Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
³⁷ Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
³⁸ Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. ³⁹ Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
⁴⁰ Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.” ⁴¹ Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
⁴² Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a. ⁴³ Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa. ⁴⁴ Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. ⁴⁵ Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. ⁴⁶ Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya, ⁴⁷ suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.