¹ Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;
zan yabi sunanka har abada abadin.
² Kowace rana zan yabe ka
in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
³ Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo
girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
⁴ Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;
za su yi magana game da manyan ayyukanka.
⁵ Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,
zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
⁶ Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro,
zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
⁷ Za su yi bikin yalwar alherinka
suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
⁸ Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,
mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
⁹ Ubangiji nagari ne ga duka;
yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
¹⁰ Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji;
tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
¹¹ Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka
za su kuma yi zancen ikonka,
¹² saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka
da ɗaukakar darajar mulkinka.
¹³ Mulkinka madawwamin mulki ne,
sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.
Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa
mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
¹⁴ Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
¹⁵ Idanun kowa yana dogara gare ka,
kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
¹⁶ Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
¹⁷ Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa
yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.
¹⁸ Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
¹⁹ Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
²⁰ Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa,
amma dukan mugaye zai hallaka su.
²¹ Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.
Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki
har abada abadin.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.