⁴ Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. ⁵ Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. ⁶ Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
⁷ An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. ⁸ Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. ⁹ Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. ¹⁰ Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. ¹¹ Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.