¹² Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon. ¹³ Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai. ¹⁴ Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa. ¹⁵ A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa. ¹⁶ Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
¹⁷ Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. ¹⁸ Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa. ¹⁹ Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. ²⁰ Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
²¹ Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane.
Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. ²² Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce, ²³ “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.” ²⁴ Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.
²⁵ Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.” ²⁶ Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.
²⁷ Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. ²⁸ Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”
²⁹ Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.