¹ In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi, ² to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa. ³ Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. ⁴ Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.
⁵ A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.
⁶ Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake,
bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,
⁷ amma ya mai da kansa ba kome ba,
yana ɗaukan ainihin surar bawa,
aka yi shi cikin siffar mutum.
⁸ Aka kuma same shi a kamannin mutum,
ya ƙasƙantar da kansa
ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa,
mutuwar ma ta gicciye!
⁹ Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri
ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,
¹⁰ don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa,
a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,
¹¹ kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne,
don ɗaukakar Allah Uba.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.