¹ Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa, ² “Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa. ³ Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi. ⁴ Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.
⁵ “Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsu fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa; ⁶ suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u; ⁷ suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’
⁸ “Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne. ⁹ Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama. ¹⁰ Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi. ¹¹ Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku. ¹² Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.