¹ Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, ² “Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba? ³ Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. ⁴ Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji. ⁵ Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji. ⁶ Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su.
⁷ “ ‘Saboda haka, ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, ⁸ Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina, ⁹ saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, ¹⁰ Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.
¹¹ “ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina. ¹² Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. ¹³ Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar. ¹⁴ Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila. ¹⁵ Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. ¹⁶ Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.