¹ Kun sani, ’yan’uwa, cewa ziyararmu a gare ku ba tă zama a banza ba. ² Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. ³ Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. ⁴ A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. ⁵ Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. ⁶ Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu.
A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, ⁷ amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. ⁸ Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. ⁹ Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.
¹⁰ Ku shaidu ne, haka ma Allah, na yadda muka yi zaman tsarki, adalci da kuma marar aibi a cikinku, ku da kuka ba da gaskiya. ¹¹ Gama kun san cewa mun bi da kowannenku yadda mahaifi yakan yi da ’ya’yansa, ¹² muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.