¹¹ Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. ¹² Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. ¹³ Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
¹⁴ An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. ¹⁵ Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan ¹⁶ dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.