⁵ Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. ⁶ Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. ⁷ Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. ⁸ A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. ⁹ Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.