¹ Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna.
(Luka 6.20-23)
Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, ² sai ya fara koya musu.
Yana cewa,
³ “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,
gama mulkin sama nasu ne.
⁴ Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu ta’aziyya.
⁵ Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,
gama za su gāji duniya.
⁶ Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,
gama za a ƙosar da su.
⁷ Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,
gama za a nuna musu jinƙai.
⁸ Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,
gama za su ga Allah.
⁹ Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,
gama za a kira su ’ya’yan Allah.
¹⁰ Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,
gama mulkin sama nasu ne.
¹¹ “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni. ¹² Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.