⁵⁷ Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka, duk inda za ka.”
⁵⁸ Yesu ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”
⁵⁹ Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.”
Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”
⁶⁰ Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”
⁶¹ Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”
⁶² Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.