Almajirai Sun Tube Tsohon, Sun Yafa Sabon

Zumunta

Game da abubuwan da suka faru da kai/ke bayan saduwar mu, menene abin da kake godiya akai?
Menene ya addabeku wannan makon, kuma me kuke bukata don abubuwa su zama da kyau?
Menene bukatun mutane al'umma ku, kuma tayyaya zamu iya taimaka wa juna biyan bukatun da muka ambata?
Menene labarin a saduwarmu na karshe? Me muka koya game da Allah da mutane?
A saduwarmu na karshe, ku yanke shawara akan yin anfani da abin da kuka koya. Me kuka yi, kuma yaya ya faru?
Wa kuka shaida wa labarin na karshe? Ta yaya suka amsa?
Mun gano bukatu masu yawa a saduwar mu na karshe, kuma mun shirya biyan bukatun. Yaya ya faru?
Yanzu, bari mu saurari wani sabon labari daga Allah...

Kolossiyawa 3: 1-17

¹ Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. ² Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. ³ Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. ⁴ Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka. ⁵ Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. ⁶ Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. ⁷ Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. ⁸ Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. ⁹ Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa ¹⁰ kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa. ¹¹ A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome. ¹² Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. ¹³ Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. ¹⁴ Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya. ¹⁵ Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya. ¹⁶ Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah. ¹⁷ Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.

Manufa

Yanzu, bari mu samu wani ya maimata wanan labari a kalmomin sa, kaman suna fadawa abokin da bai taba ji ba. Mu taimake su idan sun bar wani abu ko kuma su yi kari bisa kuskure. Inda haka ya faru sai mu yi tanbaya, " Ina ka gan wannan a cikin labarin?"
Me wanan labarin ke koya mana game da Allah, halin sa, da ayukansa?
Me mu ka koya game da mutane, har ma damu, daga labarin nan?
Me mu ka koya daga labarin nan game da zama almajirai?
Yaya zaka/ki yi anfani da gaskiya game da Allah daga labarin nan a cikin rayuwar ka/ki a wannan mako? Menene ainihin abin da zaka yi?
Wa zaka/ki shaida wa gaskiya daga labarin nan kafi mu sake haduwa? Ko ka san wadansu da za su so su gano maganan Allah a cikin wanan manhajar kamar mu?
Yayinda saduwar mu ke kamalawa, bari mu yarda lokocin da zamu sake saduwa da wanda zai jagorance mu.
Muna karfafaku ku lura da abin da ku ka ce za ku yi, kuma don sake sauraron wannan labarin a kwanaki kafin mu sake haduwa. Mai horaswa na iya bayayana labarin da ke a rubuce ko kuma a sauti, idan wani ba shi da shi. Yayinda zamu tafi, bari mu roki Ubangiji ya taimake mu.

0:00

0:00