⁸ Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
⁹ Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
¹⁰ Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki
bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
¹¹ Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
¹² Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata,
mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
¹³ Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa,
Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.
¹⁴ Shi ne Ubangiji Allahnmu;
hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
¹⁵ Yakan tuna da alkawarinsa har abada,
maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
¹⁶ alkawarin da ya yi wa Ibrahim
rantsuwar da ya yi ga Ishaku.
¹⁷ Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida,
ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.
¹⁸ “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
kamar rabon da za ka gāda.”
¹⁹ Sa’ad da suke kima,
kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
²⁰ suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
daga wannan mulki zuwa wancan.
²¹ Bai bar wani ya zalunce su ba;
saboda su ya tsawata wa sarakuna.
²² “Kada ku taɓa shafaffuna;
kada ku yi wa annabawana lahani.”
²³ Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka;
ku yi shelar cetonsa kowace rana.
²⁴ Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.
²⁵ Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;
dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
²⁶ Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
amma Ubangiji ya yi sammai.
²⁷ Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.
²⁸ Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,
ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,
²⁹ ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.
Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa;
ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.
³⁰ Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka!
Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.
³¹ Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
³² Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;
bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
³³ Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,
za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji,
gama ya zo don yă hukunta duniya.
³⁴ Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
³⁵ Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,
don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,
don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
³⁶ Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.
Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.