¹³ Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. ¹⁴ Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. ¹⁵ Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. ¹⁶ Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
¹⁷ Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. ¹⁸ Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.
¹⁹ ’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi, ²⁰ sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.