¹⁶ in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
¹⁷ Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. ¹⁸ Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata ¹⁹ ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. ²⁰ Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. ²¹ Sai dai kamar yadda yake a rubuce,
“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,
waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
“Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini.
“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.